Skip to main content

YANDA AKE HADA FUNKASO


Abubuwan hadawa
1. Filawa
2. Yeast
3. Gishiri kadan 4. Man gyada na suya
Yadda ake hadawa
1. Ki tankade filawarki ki sa gishiri kadan
sai ki ajiye a gefe.
2. Dauko yeast na ki, ki sa masa ruwan
dumi (ruwan dumi ba mai zafi ba) da suga
(karamin cokali) ki juya, sai ki rufe ki
ajiye a gefe kamar na tsawon minti 3,
idan ya na da kyau za ki ga ya yi kumfa
ya kumbura (amfanin yin hakan don ki
san yeast din mai kyau ne).
3. Sai ki juye yeast din cikin filawanki kidan kara
ruwa ki kwaba shi kamar
kwabin fanke sai ki rufe ki kai rana ya
tashi Kamar minti 20-30 idan ya taso sai
ki kara buga shi sosai ki ajiye a gefe.
4. Ki dauko kasko ki daura kan wuta, ki
zuba man gyada idan ya yi zafi, sai ki na diban
kwabin funkaso nan kadan kadan
ki na fadada shi da hannunki ki na sawa
a mai ki na soyawa har sai ya soyu, sai ki
tsane a matsani. Ana iya ci funkaso da
miyan stew, miyan taushe , Ko miyar
ganye . Aci dadi lafiya.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE YIN AWARAR KWAI

Abubuwan Da Ake Bukata: Kwai Nama Mai Maggi Attaruhu Albasa Yadda Ake Yi: Ki gyara naman ki mara kitse ki markada shi, ki jajjaga attaruhu da albasa ki juye a ciki sannan ki fasa kwanki ki kada shi kisa masa dan magi da gishiri ki juye a ciki ki juya sosai, sai ki juye a cikin farar leda ko irin ledar da ake saka bread sai ki saka a tukunya ki dafa kamar alala, in yayi ki sauke ki yayyanka kamar awara ki tsoma a kwai ki soya. Ko kuma kiyi na kwan kadai banda nama ki kada kwan kisa masa kayan hadi, ki dora ruwa ya tafasa, sai ki kawo kwan nan ki dinga tsiyayawa a cikin ruwan za kiga yana yowa sama sai kisa abin tatar awara ki juye a kai, ki daure ruwan jiki ya tsane sai ki kwance ki yayyanka ki tsoma a ruwan kwai ki soya, in za kiyi sai ki dauki daya idan kuma da hali ki gwada duka biyun.