Skip to main content

WAINAR SHINKAFA


KAYAN HADI:-
1-Shinkafa fara ta tuwo
2-Yeast
3- backing powder
4-,Suger 5-Kanwa ungurnu
Dafarko dai uwar gida zaki wanke
shinkafarki tawanku tas kibayar
amarkado miki bawai saita jiquba
anawankewa akai markade, in amkawo
sai azuba yeast da powder kadan asa suger sai
arufe akai rana,idan yatashi sai
adaiko azuba dafaffiyar shinkafa data
nuna duk da dai wasu kafin amarkado
suke zuba dafaffiyar amarkado da danyar
wasu kuma sai anmarkado suke zubawa
yadanganta da yadda mutum yake ra ayi .
sai azuba ruwan kanwa kadan ajuya sai
afara soyawa atanda idantayi ja sai
akwashe.
**ACI LAFIYA**

Comments

  1. Muna godiya sosai. Allah ya saka da alkhairi.
    Amma pls a rinka saka measurements, misali shinkafa Kofi biyu, yeast cokalin Shan shayi da dai sauransu.🙏

    ReplyDelete
  2. Muna the godiya, idan zanyi da Rana Zan iya Kai nikanta kama 9 na safe?

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

YANDA AKE HADA FUNKASO

Abubuwan hadawa 1. Filawa 2. Yeast 3. Gishiri kadan 4. Man gyada na suya Yadda ake hadawa 1. Ki tankade filawarki ki sa gishiri kadan sai ki ajiye a gefe. 2. Dauko yeast na ki, ki sa masa ruwan dumi (ruwan dumi ba mai zafi ba) da suga (karamin cokali) ki juya, sai ki rufe ki ajiye a gefe kamar na tsawon minti 3, idan ya na da kyau za ki ga ya yi kumfa ya kumbura (amfanin yin hakan don ki san yeast din mai kyau ne). 3. Sai ki juye yeast din cikin filawanki kidan kara ruwa ki kwaba shi kamar kwabin fanke sai ki rufe ki kai rana ya tashi Kamar minti 20-30 idan ya taso sai ki kara buga shi sosai ki ajiye a gefe. 4. Ki dauko kasko ki daura kan wuta, ki zuba man gyada idan ya yi zafi, sai ki na diban kwabin funkaso nan kadan kadan ki na fadada shi da hannunki ki na sawa a mai ki na soyawa har sai ya soyu, sai ki tsane a matsani. Ana iya ci funkaso da miyan stew, miyan taushe , Ko miyar ganye . Aci dadi lafiya.

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu