Skip to main content

MIYAR OGBONO


Ingredients
Nama
Kifi danye da busasshe
Ogbono
Ganda Kayan miya
Man ja
Maggi da gishiri
Curry da tafarnuwa
Preparation:
Ki tafasa namarki da gishiri, tafarnuwa, albasa, ki
soya man ja amma kadan, ki
zuba markadadden kayan miyarki a kai,
su ma ba da yawa ba, idan ya soyu sai ki
zuba dakakken crayfish kamar cokali
biyu, ki zuba busasshen kifinki da kika
gyara, ki zuba ruwa a kai, idan ta dahu sai kisa
baking powder kadan dan tayi
yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi
kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura,
shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti
biyar ko goma shike nan kingama miyarki.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.