Skip to main content

YADDA AKE ALKAKI



KAYAN HADI
1. Alkama kwano daya
2. Sugar gwangwani 6
3. Nono na shanu
4. Man shanu danye
5. Butter simas rabi
6. Mai kwalba biyu


YADDA AKE HADAWA
_Uwargida ta sheqe alkama ta cire dukkan dattin,
ko ta wanke ta baza shi a rana ya bushe. Sai ta
kai babban inji a mishi barjin fate idan aka dawo
dashi a bude tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a
juye nonon shanu, butter, man shanu, sai a murje
shi da kyau ya hade sosai. Sannan sai a zuba
ruwa amma kwabi za tayi mishi mai qarfin gaske
yanda zai hade da kyar, sai ta rufe shi ta bari ya
kwana._
_Idan ta tashi da safe sai t jiqa kanwa, ta rinqa
yayyafa masa tana hada shi tana bugawa. Har
sai ta diba a hannun ta masa nadin alkakin ta ga
bai karye ba. Wato ta yi tsaho dashi ta murza
duka bai karye ba. Kenan ba qaramin bugu zata
masa ba. Kuma ba a jibga masa ruwa sam,
yayyafa masa za ta rinqa yi tana buga shi._
_Sai ta zuba sugar a tukunya, ta zuba ruwa
kamar kofi uku ta dora a wuta. Idan mai buqatar
sugar alkakin ya rinqa diga ne bayan ya gama
shiga cikin sa sai ta saka tsamiya kwaya daya ko
(table spoon na lemun tsami) yayin da take
dafawa. In kuma tana son ya bushe a jikin sa
kamar wanda zan turo to kada ta sa._
_Wurin dafa sugar ta kula yana fara yin kumfar
farko na dahuwa ta diba a cokali yana dan fara
shan iska zata ga yayi danqo. Sai ta sauke don
haka kada ta barshi yayi ta dahuwa kamar na
tuwon madara ko aya._
_Sannan wurin soya alkakin ta saka mai aqalla
kwalba biyu ko fiye, baya shan mai sam amma
yana buqatar mai wurin soya shi. Kuma wutan
kadan-kadan yanda cikin zai soyu. Bayan ta
tsane shi a mai kai tsaye a cikin sugar zata saka,
idan tana gabda tsamewa sai ta kwashe na cikin
sugar din ta sa a kwanon da zata ajiye._
*Note:* _Idan ta yi wanda bata so sugar yana bin
sa ne zai dan rinqa daskarewa sai tana yi tana
dan narkar dashi._
_Sannan ludayin da zata rinqa amfani dashi wurin
suya daban, na sakawa a sugar shima daban._
*Wa'yanda basu iya nadin shi ba su nemi
wa'yanda suka iya su koya musu. Sannan zaku
ga wasu alkakin su yayi ja wasu sun yi haske
yanayin alkaman ne amma babu damuwa.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YANDA AKE HADA FUNKASO

Abubuwan hadawa 1. Filawa 2. Yeast 3. Gishiri kadan 4. Man gyada na suya Yadda ake hadawa 1. Ki tankade filawarki ki sa gishiri kadan sai ki ajiye a gefe. 2. Dauko yeast na ki, ki sa masa ruwan dumi (ruwan dumi ba mai zafi ba) da suga (karamin cokali) ki juya, sai ki rufe ki ajiye a gefe kamar na tsawon minti 3, idan ya na da kyau za ki ga ya yi kumfa ya kumbura (amfanin yin hakan don ki san yeast din mai kyau ne). 3. Sai ki juye yeast din cikin filawanki kidan kara ruwa ki kwaba shi kamar kwabin fanke sai ki rufe ki kai rana ya tashi Kamar minti 20-30 idan ya taso sai ki kara buga shi sosai ki ajiye a gefe. 4. Ki dauko kasko ki daura kan wuta, ki zuba man gyada idan ya yi zafi, sai ki na diban kwabin funkaso nan kadan kadan ki na fadada shi da hannunki ki na sawa a mai ki na soyawa har sai ya soyu, sai ki tsane a matsani. Ana iya ci funkaso da miyan stew, miyan taushe , Ko miyar ganye . Aci dadi lafiya.

WAINAR SHINKAFA

KAYAN HADI:- 1-Shinkafa fara ta tuwo 2-Yeast 3- backing powder 4-,Suger 5-Kanwa ungurnu Dafarko dai uwar gida zaki wanke shinkafarki tawanku tas kibayar amarkado miki bawai saita jiquba anawankewa akai markade, in amkawo sai azuba yeast da powder kadan asa suger sai arufe akai rana,idan yatashi sai adaiko azuba dafaffiyar shinkafa data nuna duk da dai wasu kafin amarkado suke zuba dafaffiyar amarkado da danyar wasu kuma sai anmarkado suke zubawa yadanganta da yadda mutum yake ra ayi . sai azuba ruwan kanwa kadan ajuya sai afara soyawa atanda idantayi ja sai akwashe. **ACI LAFIYA**