Skip to main content

MIYAR RIDI


Kayan hadi:-
√ Nama
√ Busasshen kifi
√ Ridi
√ Kayan miya
√ Alayyahu ko ugu
√ Tafarnuwa
√ Tyme
√ Maggi da gishiri
√ Kayan kamshi
√ Manja
Yadda zakiyi
Ki tafasa nama da gishiri da albasa da thyme da tafarnuwa,ki soya markadadden kayan miyarki a mai,ki zuba naman da ruwan naman a kan soyayyen kayan miyar,ki zuba maggi,gishiri da kayan kamshi,ki zuba gyararren busasshen kifinki,ki zuba dakakken kantunki kamar cikin kofi daya ko gwangwani biyu,ki rufe ya dahu kamar minti ashirin,ki yanka alayyahu ko ganyen ugu,ki wanke ki zuba,bayan kin zuva da minti biyar sai ki rage wuta miya ta yi.Zaki iya hadawa da kowanne irin tuwo

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.