Skip to main content

SPAGHETTI SALAD


Taliya
mayonnaise
peas
carrot
kwai
albasa
tumatur
vineger,butter,mai&lettuce
ki fara dafa taliyan ki wanke kana ki tsaneta,sai
ki zuba
butter dan kadan akan taliyan,ki juya sai ki ajiye
gefe.sannan ki sami carrot ki gyara shi sannan ki
grating
dinshi,ki dafa peas da dan gishiri kadan,amma
kar ki bari
ya dafe ya zama brown.sai ki sami mayonnaise ki
zuba
masa vineger kadan ki juya sosai,sai ki zuba
taiyan akai,ki
zuba carrot da peas akai ki juya sosai komai ya
hadu.sai ki
sami albasa,kwai,tumatur ki yi musu yankan
fadi,sannan ki
zuba mai a kasko kisa vineger kadan aciki sai
zuba
albasan ki soya sama sama sai ki
kwashe.Daganan sai ki
sami plate ki zuba taliyan a tsakiya ki kewaye da
yankakkun tumatur,albasa,kwai ki jera suyi
kyau.sannan ki
sami lettuce dan kadan ki wanke da ruwan
vineger kana ki
yanka shi siri siri,sai ki barbada akan taliyan don
ya bada
colour mai kyau.za'a iya cinshi zalla ko a hada
da shinkafa.
*

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.