Skip to main content

YADDA AKE YIN AWARAR KWAI

Abubuwan Da Ake
Bukata: Kwai
Nama
Mai
Maggi
Attaruhu
Albasa Yadda Ake Yi: Ki gyara naman ki mara
kitse ki markada
shi, ki jajjaga attaruhu da albasa ki juye
a ciki sannan ki fasa kwanki ki kada shi
kisa masa dan magi da gishiri ki juye a
ciki ki juya sosai, sai ki juye a cikin farar
leda ko irin ledar da ake saka bread sai ki saka a
tukunya ki dafa kamar alala, in
yayi ki sauke ki yayyanka kamar awara ki
tsoma a kwai ki soya. Ko kuma kiyi na kwan
kadai banda nama
ki kada kwan kisa masa kayan hadi, ki
dora ruwa ya tafasa, sai ki kawo kwan
nan ki dinga tsiyayawa a cikin ruwan za
kiga yana yowa sama sai kisa abin tatar
awara ki juye a kai, ki daure ruwan jiki ya tsane
sai ki kwance ki yayyanka ki tsoma
a ruwan kwai ki soya, in za kiyi sai ki
dauki daya idan kuma da hali ki gwada
duka biyun.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.