Skip to main content

*INDIAN SAMOSA*



*KAYAN HADI*

Nama
Karas
Curry
Maggi
Gishiri
Albasa
Fulawa
Attaruhu
Man gyaďa
Green beans
Baking powder
Dankalin turawa


*YADDA ZA KIYI*

Ki tankaďe fulawa sai ki zuba a roba mai faďi kisa gishiri, baking powder kaďan, ki fasa kwai a kai, da butter sai ki kwa'ba da ruwa ki buga sosai dan ya biyyu da kyau sai ki sa akan abu mai faďi ki murza yayi falai falai sannan ki yanyanka kamar (rectangle) ki ajiye a gefe, ki wanke nama ki zuba a turmi ki daka sai ki sa maggi, gishiri, albasa da attaruhu ki daďa kir'bawa sai ki zuba mangyaďa kaďan a kan wuta ki kwashe naman ki zuba a ciki kisa curry ki soya sama sama sannan ki zuba yankakken karas da green beans da kika wanke, kisa tafasashen dankalinki da kika yanyanka 'kanana, ki kwa'ba fulawa kaďan ki zuba akai dan yayi kauri ki juya da kyau idan yayi sai ki sauke, sai ki dinga ďiban haďin mai yawa kina zubawa a tsakiyar fulawarki ki ninka wani gefenshi ya zo tsakiya (kamar dai ninkin ďaurin ďan kwali) haka za kiyi tayi har ki gama ninka sauran fulawar, sai ki ďauko farantin gashi ki shafa mishi butter ki jera a ciki ki sa a oven ki gasa idan baki da oven sai ki ďora man gyaďa a kan wuta idan yayi zafi sai ki dinga soyawa in yayi brown ki kwashe har ki kammala...

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.