Skip to main content

TSIREN DANKALI DA NAMA



*KAYAN HADI*
*Dankali
*Mince meat
*Cucumber
*Tumatir
*Albasa
*Egg
*Maggie
*Spices
*Mai.
Garlic
*Kulikuli
*Yajin daddawa.

*YADDA AKE YI*
Ki feraye dankalinki sai kiyi masa yanka kamar yanda kika gani daga nan sai ki tafasashi sama sama sai ki juye a kwalanda.

Idan ya tsane sai ki soya shi sama sama again a cikin mai. Ki kwashe ki ajiye a gefe,
Ki dauko mince meat dinki ki wanke shi ki juye a kwalenda ruwan ya tsane sai ki mayar tukunya ki zuba ruwa ki saka Maggie, spices,albasa, ki daddaka tafarnuwa ki zuba akai sai ki barshi yayi ta dahuwa har sai ruwan ya kafe a jikin naman sai ki juye a abu. Idan ya sha iska sai ki dauko ki dunga yin ball dashi kanana idan kin gama sai ki saka a fridge ya kuma hade jikinsa for 15mintes.

Sannan ki dauko dankalinnan ki juyeshi a roba sai ki zuba masa dakakken kulikuli da Dan yajin daddawa ki juya ki Dan kara Maggie kadan. Sai ki daura mai akan wuta ki FASA kwai sai ki dauko naman nan da kikayi ball dashi ki dunga tsomawa a cikin ruwan kwai kina soyawa.

Dama kin yayyanka cucumber da tumatir sai ki dauko tsinken yin tsire ki soka Dankali sannan naman sannan cucumber da tumatir sannan Dankali again har ki gama. Served with hot black tea

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE ALKAKI

KAYAN HADI 1. Alkama kwano daya 2. Sugar gwangwani 6 3. Nono na shanu 4. Man shanu danye 5. Butter simas rabi 6. Mai kwalba biyu

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.

***POTATO CAKE***

Ingredients 1.Dankali. 2. Kwai 3.Tattasai 4. Albasa 5. Mai. 6. Gishiri Yadda za a yi- A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta.