*KAYAN HADI* *Dankali *Mince meat *Cucumber *Tumatir *Albasa *Egg *Maggie *Spices *Mai. Garlic *Kulikuli *Yajin daddawa. *YADDA AKE YI* Ki feraye dankalinki sai kiyi masa yanka kamar yanda kika gani daga nan sai ki tafasashi sama sama sai ki juye a kwalanda. Idan ya tsane sai ki soya shi sama sama again a cikin mai. Ki kwashe ki ajiye a gefe, Ki dauko mince meat dinki ki wanke shi ki juye a kwalenda ruwan ya tsane sai ki mayar tukunya ki zuba ruwa ki saka Maggie, spices,albasa, ki daddaka tafarnuwa ki zuba akai sai ki barshi yayi ta dahuwa har sai ruwan ya kafe a jikin naman sai ki juye a abu. Idan ya sha iska sai ki dauko ki dunga yin ball dashi kanana idan kin gama sai ki saka a fridge ya kuma hade jikinsa for 15mintes. Sannan ki dauko dankalinnan ki juyeshi a roba sai ki zuba masa dakakken kulikuli da Dan yajin daddawa ki juya ki Dan kara Maggie kadan. Sai ki daura mai akan wuta ki FASA kwai sai ki dauko naman nan da kikayi ball dashi ki dunga tsomawa a cikin ruwan kwai kina soyawa....