Skip to main content

Posts

Showing posts from 2020

TSIREN DANKALI DA NAMA

*KAYAN HADI* *Dankali *Mince meat *Cucumber *Tumatir *Albasa *Egg *Maggie *Spices *Mai. Garlic *Kulikuli *Yajin daddawa. *YADDA AKE YI* Ki feraye dankalinki sai kiyi masa yanka kamar yanda kika gani daga nan sai ki tafasashi sama sama sai ki juye a kwalanda. Idan ya tsane sai ki soya shi sama sama again a cikin mai. Ki kwashe ki ajiye a gefe, Ki dauko mince meat dinki ki wanke shi ki juye a kwalenda ruwan ya tsane sai ki mayar tukunya ki zuba ruwa ki saka Maggie, spices,albasa, ki daddaka tafarnuwa ki zuba akai sai ki barshi yayi ta dahuwa har sai ruwan ya kafe a jikin naman sai ki juye a abu. Idan ya sha iska sai ki dauko ki dunga yin ball dashi kanana idan kin gama sai ki saka a fridge ya kuma hade jikinsa for 15mintes. Sannan ki dauko dankalinnan ki juyeshi a roba sai ki zuba masa dakakken kulikuli da Dan yajin daddawa ki juya ki Dan kara Maggie kadan. Sai ki daura mai akan wuta ki FASA kwai sai ki dauko naman nan da kikayi ball dashi ki dunga tsomawa a cikin ruwan kwai kina soyawa....

FRIED IRISH

    🥔🥔FRIED IRISH🥔🥔 *Abubuwan bukata* *🥔Irish* *🥔Kwai* *🥔Attaruhu* *🥔Tumatur* *🥔Albasa*             _Kufere dankalinki kiyankashi yadda kike bukata kiwanke sai kidora manki awuta idan yayi zafi kijuye dankalinki kisoyashi idan yasoyu ajiye agefe kidora fan dinki awuta kizuba mai kadan badayawaba idan yayi zafi kifasa kwanki kwaya daya batareda kinkada kwanba ahakan gudanshi kijuye idan yasoyu kijuya dayan barin ahakan har kiyi adadin kwan dakike bukata zakiga kwan yayi kamar wainar kwai kamar kuma dafaffe kidora tukunyarki awuta kizuba mai kadan juye jajjagenki kada kisakawa jajjagen ruwa kisaka dan dano gishiri da kayan kamshi kiyanka kwanki wanda kikasoya kananu kijuye acikin source dinki tareda soyayyen dankalin kirufe suturara akwai dadi sosai😋😋😋_

YADDA AKE SPRING ROLLS

*ingredients* Cabbage Carrots Onions Flour Eggs Minced meat Oil Curry Maggi&spices       *method* Ki hada flour, kwai maggi gishiri da ruwa a kwaba yayi kamar kwabin wainar flour sai ki shafa mai a non-stick pan dinki( idan bakida non stick sai ki shafa pan dinki da gishiri amma idan kina da nonstick no need of shafa gishiri) sai ki dauko brush ki shafa wannan kwabin naki a pan din idan yayi zakiga gefen ya dago sai dauko haka zakiyi for the while dough.      *filling* Ki yanka cabbage da onions da carrots ki soya samasama tare da mai cokali daya ki zuba minced meat dinki maggi da sauran spices sai ki sauke sai ki dauko wannan flour da kika gasa kiyi filling a gefe daya sai ki nade kamar tabarma sai kisa kwabin a edges din yayi serving as gum dan kar ya bude wajen soyawa. *NOTE* anason man suyan ya zama da zafi sannan a zuba in ba haka ba zai sha mai kuma bazai zama crispy ba.